Qilu Taja Bau
Wata rana, budurwa wani saurayin ta je wurinsa hira da suka gama hirar dare yayi sai ya tafi zai raka ta to ita wannan budurwa tana zaune a wani kauye ne ba kauyen da saurayin yake ba. To a tsakanin kauyukan nasu akwai wani daji da wani kogi ya ratsa. Da suka zo wannan kogi sai saurayin yace wa budurwan ta dakata yayi iyo cikin ruwan ya haura daya bangaren kogin ya dauko kwalekwale don ya haye da ita. Sai ya shiga ruwan. Yaje tsakiya kenan saiga wani gawurtaccen kada ya taso masa yana takai masa cafka. Da kyar ya haye. Yana hayewa ya waigo baya cikin farin wata sai ga wata damisa ta tsare yarinyarsa tana ta kai mata hari yarinyar na ihu. Ya dubo cikin ruwan kuma yaga kada ya dago baki yana jiran sa. To wai idan kaine yaya zaka yi????
Tags:

0 comments: