Saturday, 4 April 2015

DUNIYA MAYAUDARIYA CE

DUNIYA MAYAUDARIYA CE

Karka damu da Qyale-qyalen duniyarnan domin mayaudariyace, idan kasan haqiqanin siffofin yaudara to, duk wannan mata (duniya) ta siffantu da su.

Itace fa mai Qunshe da dukkan wani nau'i na Qazamta da dagwalon datti, amma a ganin ido (ga duk wanda ya
jarabtu da son ta) ganin ta yake yi koriya shar gwanin ban sha'awa.

Qamshi gare ta tamkar turare ga duk wanda ta rud'a! Amma kuma d'aci gare ta tamkar guna ga duk wanda
yayi watsi da ita.

Lallai duniya wata kasuwa ce ta neman ribar samun annashuwa da walwala tare da ni'imomi a gidan haqiqa wato (Lahira), duk wanda ya mu'amalance ta a haka shine wanda zai fa'idantu da ita.

Wanda ko ya d'auketa madawwama wurin tuturta! To, wannan kam zai sha mamaki, don kuwa sai ta gama
sab'a shi sama kowa ya ganshi sannan ta mako shi Qasa.

Ashe mai wayo da hangen nesa, tare da sanin ya kamata gami da dabara shine wanda zai d'auki rayuwa a duniya tamkar wanda ke cikin jirgin ruwa ne acikin kogi kuma yake son Qetarewa, kaga babu wata alaqa tsakanin shi da kogin nan face, yayi anfani dashi wajen samun damar
Qetarewa.


Allah ya bamu ikon fa'idantuwa da wannan gida ta hanyar gyara rayuwar dake tafe wato rayuwa a gidan lahira, ya bamu ikon watsi da duk wani abu dake rud'i game da hanyar Allah a duniyar nan, ya kuma sa mu zamanto masu haqiqanin neman yardar Allah.
(Ameen)
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: