KU DUBI WANNAN ALFARMAR
Ibnu Katheer ya kawo acikin Tafseerinsa cewa: Imamul Utbiy (rah) yace:
"Na kasance ina zaune awajen Qabarin Manzon Allah (saw) sai ga wani Balaraben Qauye ya shigo. Sai yace:
"ASSALAMU ALAIKA YA RASULALLAHI! Hakika ni naji Allah yana cewa : "DA ACHE SU (MUTANE) IDAN SUN ZALUNCI KANSU (SUN AIKATA ZUNUBI) ZASU ZO GAREKA, SU NEMI GAFARAR ALLAH, KUMA MANZON NAN YA NEMA MUSU GAFARA, DA SUN SAMU ALLAH MAI KARBAR TUBA NE, KUMA MAI JIN QAI".
Don haka ganin nan nazo gareka ina neman gafarar Zunubina, Kuma ina neman ceto dakai awajen Ubangijina".
Sannan sai shi (balaraben kauyen) ya sa'bi baitukan waqar Yabon Manzon Allah (saww) yana cewa:
"YA MAFIFICIN WANDA AKA BINNE JIKINSA ACIKIN QASA, SAI QASSAI DA TUDDAI SUKAYI DA'DI DA QAMSHINSU.
RAI NA FANSA NE GA QABARIN NAN DA KA KASANCE KAI NE MAZAUNIN CIKINSA. ACIKINSA AKWAI WADATUWA, DA KUMA KYAUTA DA KARAMCI".
Sannan sai Balaraben Qauyen ya juya ya fita. Ni kuma sai idanuwa na suka rinjayeni nayi barci. (Acikin barcin) Sai naga Manzon Allah (saww) yace min :
"YA KAI UTBIY, JEKA KA RISKI WANNAN BALARABEN QAUYEN. KAYI MASA BISHARAR CEWA ALLAH YA RIGA YA GAFARTA MASA".
Aduba :
* Tafsirin Ibnu Katheer, Juzu'i na 1, Shafi na 691. Da juna Juzu'i na 4,.shafi na 140. karkashin ayah ta 64 acikin Suratun Nisa'i.
* AL-AZKAR na Imam Nawawiy juzu'i na 1 shafi na 440.
Wannan Hadisin yana isharah ne zuwa ga Girman matsayin Manzon Allah (saww) da kuma halaccin yin kamun Qafa dashi domin neman gafara da kuma ceto awajen Allah.

0 comments: