Saturday, 10 October 2015

SIRRIN DA SHAITAN YA BAWA ANNABI NUHU

SIRIN DA IBLIS YA BAWA ANNABI NUHU (AS)..

Yazo a cikin littafen KHISAL cewa a lokacinda Annabi Nuhu (as) yayi Addu'a aka Hallaka Duniya gabadayan ta,banda muminan da suka hau jirgi a tare da shi, Sai Iblis (l.a) yazo wajen Annabi Nuhu (as) yace:

Ya Nuhu Haqiqa kayi min Abin Arziqin da ya faranta man, dan haka ina so inyi maka wani Tagomashi a matsayin ladar kyautatawar da Kayi man.

Sai NUHU (as) yace da shi: Amma kuwa zan ji Haushin ace Nayi Aikin da zai faranta maka (Ya maqiyin Allah) to menene nayi wanda faranta maka??

Sai Iblis yace:

Kayi Addu'a Allah ya hallaka mutanen ka masu sabo, can da ina ta famar ingiza su kan su bijire maka, su kuma sabawa Allah, inyi wannan makirci, in kulla wanna gadar zare, domin dai in tabbatar da basu Musulunta ba, Amma yanzu da kayi Addu'a aka Hallaka su sai na huta, yanzu ba wani mutum da zan batar, duk sun mutu a DUFAN, sai dai in jira har wasu Al'ummomi suzo sannan in cigaba da batar da su.

Sai Nuhu yace da shi: To wani tagomashi ne kake cewa zaka sakanta man da shi??

Sai yace da Nuhu:

Ka Tuna ni a wurare guda uku saboda nafi zama kusa da mutum a wadan wurare guda uku:

1. A lokacin fushi (zan riqa ingiza mutum har takai ya iya yin kisan kai)

2. A lokacin da bawa zaiyi Hukumci tsakanin mutum biyu.

3. A lokacin da Namiji ya kebanta da mace su kadai ba mai ganin su.

To ya NUHU ka kiyayi wadannan wuraren guda uku domin a nan ne nafi dana tarko na.

ALLAH KAIMANA TSARI DA SHAIDAN.

Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: