KAURA ZUWA HABASHA (ITOFIYA) .
Cutarwan mutanen Makka ga musulmai sai kara tsnanta yake ga mabiya Muhammad (SAW), mafi yawan musulmai sun kasance wadanda ake muzguna musu da barazanan kashe su. Don haka Muhammad (SAW) ya umurce da suyi kaura zuwa kasashen duniya irin su Habasha. .
Da suka tambaye shi ina ya kamata su fara zuwa sai ya basu shawarin zuwa ga sarkin Habasha (Itofiya) saboda masarautan kiristanci ne, ‚Saboda dukkan garin da sarkinsu ke da addini to lallai tsarin gudanarwansu zai zamo mai adalci saboda tsoron Ubangiji.‛ Tsoron cutarwan mutanen Makka da matukar son bauta wa Ubangiji yadda ya kamata ya sanya su neman yin kaura don su bauta wa Ubangiji cikin ‘yanci. .
Don haka wasu adadi daga cikin Musulmai suka yi kaura zuwa Habasha (Itofiya), jama’a ta farko mutum goma sha daya ne, da mata hudu. .
Bayan sun fita garin Makka a boye suka isa garin Habasha in da suka zauna a karkashin kulawar sarki Najjashi ba su koma ba face lokacin da suka sami labarin cutarwan kuraishawa ya ragu ga musulmai a garin Makkah. .
Da suka komo kuma sai cutarwan kuraishawa ya karu fiye da ta farko, sai suka sake kaura zuwa Habashi karo na biyu, a wannan lokaci kamar mutum tamanin suka yi kaura banda mata da yara. Wadannan jama’an musulmai haka suka yi ta zama a Habasha har sai da Muhammad (SAW) ya yi kaura zuwa Yathriba (Madina). Kuma kauran musulmai zuwa kasar Habasha ita ce aka rubuta cewa, ‚kaura ce ta farko a Musulunci.

0 comments: