MUSULUNTAR HAMZA (RA)
Babban martaba da matakin ci ga wanda ya faru ga Muhammad (SAW) da mabiyansa shine abin da ya jawo hankalin Banu Hashim da Banu Abdul Mudallabi suka kara goya mashi baya kuma tare da ba shi tsaro. .
Wani abu da ya shiga kundin tarihi shine wata rana Muhammad (SAW) yana tafiya a wata hanya, sai Abu Jahali ya zage shi kuma ya zagi sabon addini. Muhammad (SAW) bai amsa mashi da komai ba, ya tafi abin sa. .
Hamza baffan Muhammad (SAW) kuma dan uwansa wajen shan nono, yana kan addinin kuraishawa kuma jarumi kakkarfa, kuma mafarauci ne, in ya komo daga rangadinsa sai ya yi dawafi a Ka’abah kafin ya shiga gidansa. .
Ana haka ne ya shigo lokacin da Abu Jahali ke zagin Muhammad (SAW) kuma ya fahimci abin da ke faruwa a tsakaninsu da dan dan uwansa. Sai ransa ya baci ya tafi kai tsaye zuwa ga Ka’abah, da shigan shi Masallacin, bai kula da kowa ba kamar yanda ya saba yi kullum, face sai ya doshi Abu Jahali ya doke shi da bakansa. .
Sai wasu manya daga kabilar Banu Hashim suka mike don taimakon Abu Jahali. Amma Abu Jahali har ya na ture su gefe. Sai ya fahimci saboda ya zagi Muhammad (SAW) ne, haka ta faru da shi, don haka bai bar maganan nan ta kara wastuwa ba, don haka shi yafi mashi alheri akan Banu Hashim suji abin da ya faru.
Daga nan dai Hamza ya bayyana shigar sa addinin Musulunci kuma ya yi rantsuwan kare dukkan abin da zai faru da Muhammad (SAW). Kuma ya yi alkawarin bada rayuwansa gaba daya domin Allah.

0 comments: