Wednesday, 7 October 2015

MARAICIN MANZO (S.A.W)

MARAICIN MANZO (S.A.W)

Jika ya zamo wani abu mai matsayi da ake kauna fiye da yadda ake daukar kakan. Daga nan sai Amina ta dauke shi zuwa garin Madina don ziyarar kawunensa na kabilar Najjar. .

A lokacin tafiyar ta ce, ta tafi da Ummi Aimana baiwar mijinta da ya mutu ya bari. A garin Madina Amina ta nuna mashi gidajen kawunensa da gidan da mahaifinsai ya mutu wato ta nuna mashi kabarinshi (mahaifinsa). Wan nan ya zamo abu na farko da yaron nan ya fara gani na maraici kuma ya tabbatar da cewa, shi maraya ne, uwar ta bayyana mashi komai game da matsayin mahaifinsa lokacin da ya rabu da ita a bayan ‘yan kwanaki kadan da yin aurensu a inda ya biyo garin Madina kuma ya mutu anan. .

Bayan kauranshi Muhammad (SAW) zuwa wannan gari, sai ya bayyana ma sahabbansa farko ziyaransa ga garin, bayan watanni Amina ta komo daga Madina zuwa Makka da danta ta hawo da rakuma biyu da ya dauke su zuwa can, da ga isowarsu Abwa’u sai ciwo ya kama Amina a wannan kauye harta mutu aka binne ta. Ummi Aimana ce, ta komo da yaron nan zuwa garin Makka wanda ya kasance cikakken maraya (ba uwa ba uba).

Kamar yanda uwarsa tayi fama da bakin cikin mutuwar mahaifinsa shima kuma ga shi ya sake shiga irin wadda ta shiga don ta ba shi labari wannan, ya sanya shi samun kansa cikin halin na farkawa da dukkan abin da zai ci karo da shi a rayuwa.

Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: