Monday, 12 October 2015

MUSULUNTAR UMAR DAN KHADDABI

MUSULUNTAR UMAR DAN KHADDABI (RA)

. A wan can lokaci Umar dan Khaddabi yana da karfin kuruciya, na da kamar shekaru talatin zuwa talatin da biyar. Kuma ya tashene da karfin kuriciya da jarunta ka. Kuma shi Umar dan Khaddabi rayuwansa kenan a halin nuna karfi, kuma yana so kayan maye (giya) da abubuwan ban dariya wannan ke rage mashi bakin halin rayuwa. . Amma duk da haka mutum ne mai mutunci da martaba kuma na son jama’a. Don haka ya musulunta ya zamo babban jarumi (jarumi) wajen kare su daga abokan gaba, marar tausa yi wajen dawwamar da zaman lafiya, da bayar da tsaro ga addini. .

Saboda haka kauran da Musulmai suka yi zuwa Itofiya da zama karkashin kulawar Najjashi ya rage mashi jin haushin (su). Saboda yana alfahrin shi mazaunin Makka ne kuma haka yana mashi ciwo har wani sarki na wata kasa na taimaka wa mutanen Makka wanda basu da kyakkyawan tsaro ko zaman lafiya a garinsu. Muhammad (SAW) wata rana ya hadu da mabiyansa a wani gida da ake kira Saffah yanki daya cikin hudu na garin Makka daga cikin wadanda suka halarta akwai kawunsa Hamza, da dan dan’uwansa Aliyu dan Abi dalib, da Abubakar dan Abi kuhafah da dai sauran Musulmai. Sai Umar ya ji labarin taronsu sai ya fuskanci zuwa wurin don ya kashe Muhammad (SAW) kuma haka zai rage wa kuraishawa nauyin da ke kansu. Kuma haka zai kara hadin kansu, kuma zai tabbatar da martabanta a wajen gumaka wanda Muhammad (SAW) ke aibatawa. .

A hanyarsa ta zuwa Makka sai ya hadu da Nu’aimi dan Abdullah, kuma da ya fahimci abin da Umar ya ke nufi, sai Nu’aim ya ce: ‚Ina rantsuwa da Ubangiji! Kana cutar kanka ne, Umar! Kana ganin kabilar Abdu Manaf ba za su yi ca akanka ba. Idan ka kashe musu da ba wato Muhammad? Kuma me zai hana ka koma zuwa gidanka, ka daidaita su (don kuwa ‘yar uwansa Fadima ta musulunta).‛ Da Umar ya fahimci Fadima ‘yar uwarsa da mijinta Sa’id dan Zaid sun riga sun shiga Musulunci, sai ya koma zuwa gidan kai tsaye ya iskesu. .

Da shigar shi gida bai kwankwasa ba, sai ya iske daya daga cikinsu na karanta Alkur’ani; gaba dayansu suka ji shigarsa, sai suka fara buya ga bakon, suka boye takardun Alkur’ani wanda suke karantawa. .

Umar ya tambaya: ‚Wani abune naji kuke karantawa, lokacin da nake shigowa?‛ Biyu daga cikinsu suka musunta cewa, babu komai da ya ji saboda tsoron abinda Umar zai aiwatar akansu; Umar ya ambata musu cewa, ya ji sun shiga wani sabon addini kuma sun shiga addinin Muhammad (SAW) ne, saboda haka ya zungure su, ya fara kaiwa musu bugu (duka) mai karfi ga dan uwan surkinsa Sa’id. .

Sai Fadima ta mike don kare mijinta, ta tsaya a tsakanin mutum biyu, Umar ya doke ta akai har sai da ta fara zuban jini. Daga nan biyu daga cikinsu tsoro ya gushe daga gare su gaba daya, suka ce, ‚Lallai haka ne, mu zamo Musulmai! Ka aitaka dukkan abin da kake son aikawa.‛ Saboda nuna rashin tsoron da suka yi ga Umar kuma ya ga kan ‘yar uwansa na zuban jinni sai ya fita. Daga baya ya koma ya roki ‘yar uwansa da ta nuna mashi takardun wadda ita da mijinta suke karantawa tare; bayan ta mika mashi takardun, sai ya karanta nan take fuskarsa (kamanninsa) ta fara canzawa saboda bakin cikin abin da ya aika ta. .

Da ya kare karatun takardun nan sai ya firgita mai zaurfi saboda kyawon abin da ya karanta da martabanta kuma da abin da ke koyarwa, kuma saboda tasirin abin da sakon ya kunsa. Daga nan Umar tunaninsa na kyawo ya fara gaya mashi gaskiya. Sai ya bar gidan ‘yar uwansa, zuciyarsa tana cike da doguwar tunani. Kuma ransa ta fara darsa mashi yarda da sabon ban gaskiya da bayyanar shi gare shi; sai ya tafi kai tsaye zuwa ga Saffahin da Muhammad (SAW) yake ganawa da mabiyansa, don neman yanda zai shiga wannan addinin. .

Nan take Umar ya bayyana karban musuluncinsa a gaban Annabi (SAW). Musulmai sun yi farin ciki da mamaki game da shigar shi Musulunci saboda karin karfin da suka samu ga Hamza, kuma ga wani sabon tsaro ya karu cikin al’umma ta gaba daya. Musuluntar Umar ya kara raba kan kuraishawa fiye da yadda suke a baya kuma haka ya rage musu karfi kuma ya rage musu samun matsayin gudanarwa. Kuma haka ya kara wa Musulunci karfi babba; kuma haka ya sanya shi (Musulunci) tasiri wanda su da kuraishawa ko wane zai kara canza matsayinsa, gaba da gaba. .

Haka ya samar da wata sabuwar hanya na gudanar da addini kai tsaye da kuma sadaukarwa na sabuwan tsaro ga dukkan wadanda suka yi kaura ga Muhammad (SAW) kuma ya samar da sabuwa siyasar a wani bangaren yada da’awarsa.

Previous Post
Next Post

About Author

1 comment: