Wednesday, 7 October 2015

RAYUWAR MANZO (S.A.W) A HAMADA

RAYUWAR MUHAMMAD (SAW) A HAMADA .

Har kusan shekaru biyar Annabi (SAW) ya yi rayuwa a hamada cikin kabilar Banu Sa’ad yana shakar iskar hamada kuma ga ‘yancin rayuwa na mutanen kauye. Nan kuma ya koyi harshen larabci don mutanen kauye sunfi tsare asalin harshe wanda ke daidaito ga jama’ar gari. Saboda haka masana tarihi sunce Muhammad (SAW) ya taba cewa, ‚Nine fiyyayyen balarabe a cikin ku don ina daga cikin kabilar kuraishawa, kuma na taso ne daga kabilar Banu Sa’ad dan Bakar,‛ wannan a bangaren tarihi muka dauki wannan don kuwa akwai maganar da ta fito daga bakinsa da wani lafazin da ba wannan kuma tafi shahara Allah ne Mafi sani. .

Shekaru biyar da Muhammad (SAW) ya yi a kabilar Banu Sa’ad ya kara musu wadata da daukaka Halima da makwaftanta kuma sun yi matukar sonsa a dukkan rayuwansa haka abin da ya biyo baya a wajen aurensa da Khadija har Halima sai da ta ziyarci Muhammad (SAW), ta komo gida da kyautar rakumi dauke da kayansa da garken shanu arba’in. Duk lokacin da Halima ta ziyarci Muhammad (SAW) ya kan girmama ta, kuma yana nuna matsayinta ga mutane, wata rana Shaima diyar Halima an taba kamata a bauta lokacin yakin Musulunci tana bangaren kabilar Hawazinawa da aka ci da’ifa da yaki. .

Da aka zo da ita ga Muhammad (SAW) ya gane ta, sai ya tarbe ta da mutunci, ya aika ta ga mutanenta sa’adda ta nema haka gare shi. Muhammad (SAW) na kuruciyarsa dan shekara biyar aka komo da shi wajen mahaifiyarshi. .

Wannan ya raba tsakanin Halima da Muhammad (SAW) saboda komowarshi garin Makka ya zauna ga Abdul Mudallabi. Wata rana Abdul Mudallabi ya bincika a nemo shi (Muhammad) sai aka iske shi wajen Waraka dan Nawfal (wani babban malamin a addinin Isah labarinsa na nan zuwa lokacin wahayi). Daga nan Abdul Mudallabi ya dauki nauyin lura da jikansa kuma ya zamo mashi abin da ya fi so don kuma ya kasance shine jagoran kuraishawa a fadin Makka gaba daya. Sai ya rika daukansa yan zuwa da shi ya shimfida a inuwar dakin Ka’abah, sauran yaransa na kewaye da shi. Daga kazo zaka fahimci banbancin matsayin yaron akan shimfida saura na zaune kasa. . Haka Muhammad (SAW) ya rika walawa a lokacin da ke karkashin kulawar kakansa kuma ya kan barshi ya zaga dukkan kawunayensa na wajen uwa da uba.

Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: