Thursday, 9 October 2014

BABBAN ARZIKI !

Duk wanda Allah ya azurta shi, da samun abu biyar, a rayuwarsa, yayi babban arziki.

Na daya: biyayyya ga umarnin Allah, idan yace ayi to ka tashi kayi, iyawarka, domin Allah kuma akan sunnah.

Na biyu, : idan Allah yayi hani ka hanu, domin hanuwar shine arzikin ka duniya da lahira,

Na uku,: Idan Allah ya baka kayi godiya, da gabbanka da zuciyrka da bakinka, kuma ka aiwatar da ita ta hanyar da ta dace,

Na hudu,: Idan Allah ya jarrabeka kayi hakuri, ka mayar da komai ga Allah,

Na biyar,: Idan kayi laifi, ka tuba, kayi nadama da istigfari.

Allah yasa mu dace.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: