Soyayyar Shinkafa Mai Kwakwa
Assalmu alaikum makaranta wannan shafi, ya aka ji da hidimomin yau da kullum. A yau muna dauke ne da yadda ake yin soyayyiyar shinkafa mai kwakwa. Na san yawancin uwayen gida sun san yadda ake yin soyayyiyar shinkafa. A nan na kara da kwakwa ne domin girkin ya fi dadi da armashi.
KAYAN DA ZA KI TANADA
1. Shinkafa
2. Karas da fis(peas) da albasa
3. Bota(butter)
4. Madarar kwakwa(coconut milk)
5. Kifi (shrimps)
6. Hanta
7. Man zaitun
8. Gishiri da dunkulen knorr
9. Kori
10. Kwai
YADDA ZA KI DAFA KI SOYA
Ki sami shinkafarki ki wanke sosai da ruwa mai kyau. Ki zuba ruwa a tukunya, idan ya tafaso sai ki zuba wannan shinkafar, idan ta yi kamar rabin dahuwa sai ki sauke ki wanke ta da ruwa sosai. Sai ki kara mayar da ita kan wuta , ki kawo madarar kwakwa ki zuba akan shinkafar da dan gishiri dan kadan. Ki rufe tukunyar, ki kuma rage wutar har sai ta dahu , ba dahuwa ligif ba. Sai ki samu wata tukunyar ki wanke hanta sosai ki zuba a cikin tukunya da ruwa dai- dai yadda zai dafa hantar ta yi laushi. Ki zuba gishiri da dunkulen knorr da albasa da dan kori, sai ki rufe tukunyar ki bar hantar ta dahu. Idan hantar ta dahu sai ki sauke ta daga kan murhu, ki yanka ta kananu. Ki sami albasa babba ki yanka ta, ki kankare karas ki yanka shi, ki wanke fis din ki hada su wuri daya. Ki dora kaskon suya a kan wuta ki zuba mai a ciki, idan ya yi zafi sai ki zuba wannan hantar da kika dafa, ki zuba kifi (shrimps) a ciki da albasa da fis da karas ki yi ta juyawa har sai kin ga wannan kifin ya fara kamar ja. Sai ki kawo shinkafarki da kika dafa ki zuba akai, ki zuba gishiri da dunkulen knorr da kori ki juya. Sai ki kawo bota ki zuba. Ki cigaba da juyawa kamar minti biyar. Za ki ji kamshin wannan botar ya game ko ina, idan kin ci kuma za ki ji dadin abincin ya karu. Idan kina so kina iya saka kwai a ciki. Ki sami kwai ki fasa, ki cire kwanduwar sai ki soya, idan ta dauko soyuwa sai ki saka cokali ki ragargazata ki cigaba da juyawa har sai ta soyu. Idan ta yi sai ki zuba a kan wannan shinkafar da kika gama hadawa ki juya.
Kina iya cin wannan soyayyiyar shinkafar ita kadai, idan kina so kuma kina iya ci da da miya.
KOSAN DANKALI DA KAZA
KAYAN DA ZA KI TANADA
1. Kaza
2. Dankalin turawa
3. Albasa da attaruhu
4. Gishiri da dunkuen knorr
5. Kwai
6. Kori
7. Man gyada
YADDA ZA KI HADA
Ki sami kaza ki dafa ta da albasa mai yawa da gishiri da dunkulen knorr, ki zuba ruwa isashshe yadda za ta dahu ta yi laushi sosai. Ki feraye dankalin turawa shi ma ki dafa shi ya dahu ligif. Idan ya huce sai ki saka hannu ki marmasa shi, ki kawo wannan kazar ita ma ki cire duk kashin da yake jikinta ki marmasheta ki zuba a kan dankalin. Sai ki jajjaga attaruhu da albasa a turmi, ki zuba shi a kan wannan kaza da dankalin turawa, ki kawo kori ki zuba, ki kara gishiri da dunkulen knorr dai-dai dandano ki juya sosai. Ki sami kwai ki fasa,ki kada shi sosai sai ki juye a kan wannan hadin dankali da kazar. Ki juya sosai domin komai ya ji. Idan kin gama sai ki ringa diba kina mulmulawa kamar kwallo dai-dai yadda kike so. Idan kin gama sai ki saka shi a cikin firinji ya yi kamar minti goma, domin ya hade jikinsa, idan kuma babu wuta ko babu firinjin kina iya ajiye shi a waje ya dan sha iska. Ki dora mai a kasko ki bari ya yi zafi, sai ki ringa sakawa a cikin man, idan bari daya ya soyu sai ki juya daya barin ma soyu. Haka zaki yi ta yi har ki gama soya duka.
Aci dadi lafiya!
AJIYAR DANYAR KUBEWA
Idan ke irin matan nan ne da suke son su sayi kayan miya da yawa su ajiye to ga hanyar ajiye danyar kubewa ta dade miki ba tare da ta lalace da wuri ba. Wasu matan sun fi son sayen kayan miya da yawa su ajiye,ba kullum sai an je kasuwa an siyo ba. Haka kuma idan da hali kuma da wadatar hakan ya fi sauki ki sayi kayan miyarki da yawa ki ajiye, ya ma fi arha.
Idan kin siyo kubewa da yawa sai ki wanke ta sosai ki goga a magogi, sai ki juye ta a cikin tukunya, ka da ki saka gishiri ko ruwa, kubewar kawai zaki zuba, ki juya ta har sai kin gat a fara turiri, turiri ya rufe tukunyar, amma ba dahuwa ba. Sai ki sauke ta daga kan wuta, ki bari ta huce, sai ki kawo leda ki zuzzuba ta a ciki ki saka a cikin firiza. Duk lokacin da kika ta shi amfani da ita sai kawai ki ciro daga cikin firizar ki bari ya huce sannan ki yi amfani da ita. Kuma ta kan yi watanni a cikin firizar ba tare da ta lalace ba. Idan kin dafa kuma baza ta canza kala ta yi baki din nan ba, haka kuma ba ta yin wannan ruwa-ruwa din kamar wadda kike sakawa a cikin firinji. Asha miyar kubewa lafiya.
GIRKINKI SIRRINKI
Tags:
soyayya Zallah

Munajin dadi
ReplyDeleteTaya zan seta fecebook dina
ReplyDelete@Zee fation ,
ReplyDeleteMe yake miki