GWARZON MUSULUNCI, SALMANUL FARISIY (RA) - KASHI NA 2
Salamanul farisy ya tambayi Malaminsa cewa yana so yasan alamomin da zai gane wannan Annabin Qarshr din dasu.
Sai Malaminsa yace masa: "Yana cin kyauta amma ba ya cin sadaka. Sannan kuma akwai Hatimin Annabta abayansa (ko bayan kafadunsa). Kayi sauri kaje ka riskeshi domin yanzu haka ma ya kusa yin hijira zuwa wani gari mai dabinai (Wato Yathrib ko Madina).
Daga nan sai wannan Malamin ya rasu, shi kuma Salmanul Farsiy yaci gaba da zama agarin yana yin sana'a yana tara kudi har sai da ya zama mai arziki sosai.
Rannan sai ya samu labarin cewa akwai wasu larabawa sunzo Fatauci, amma zasu koma ta wajen garin nan mai dabinai (wato madinah).
Don haka yaje ya samesu yace musu ZAI BASU DUKKAN DUKIYAR DA YA MALLAKA, HAR GARKEN SHANUNSA DA RAKUMANSA, IN DAI ZASU KAISHI GARIN YATHRIBA (MADINA).
Suka amince suka karba. Amma da suka zo kusa da kauyukan Yahudawan Madeenah sai suka kama Salmanul Farisiy suka sayar dashi, suka ce wai bawansu ne.
Nan ya zauna yana ta aikin bauta ahannun wani bayahude. Rannan yana kan bishiyar dabino yana yima Maigidansa aiki sai yaji wani Dan uwan maigidan yazo yana gaya masa cewa: "Wai kaga larabawan nan duk sun tafi wajen wani mutum bako, wanda yazo daga Makkah, yace musu wai shi Annabi ne".
Salmanul Farisiy yana jin wannan maganar sai jikinsa ya fara rawa, gaba daya ya rikice, ya sauko afirgice... Yace ma Mutumin "A ina wannan Annabin yake? ".
Nan take sai Ubangidan nasa ya mareshi da Qarfi.. Yace masa "Kai amatsyinka na bawa, ina ruwanka da maganar Annabta? "
Salamanul Farisiy yaci gaba da bincikar gaskiya labarin nan, har dai aka tabbatar masa cewa Manzon Allah (saww) yayo hijira daga Makkah ya taho Madeenah, kuma yanzu haka ma yana nan a Quba' (wani waje ne kusa da Madeena).
Don haka ya samo dan wani dabino ya tafi dashi chan Quba. Ya tarar da Manzon Allah (saww) atsakiyar Sahabbansa, Sai ya miko wannan dabinon yace masa "GA SADAQAH".
Manzon Allah (saww) bai ci ba, sai ya mika ma Sahabbai yace musu "Kuci, domin ni bana cin Sadaqah".
Salmanul Farisy sai yace "Naga ta farko kenan daga cikin alamomin nan".
Watarana kuma sai ya sake kawowa wani dabinon ya mika ma Manzon Allah (saww) yace masa "GA KYAUTA". sai Manzon Allah (saww) ya mika hannu ya karba ya fara ci tare da Sahabbansa..
Sai Salmanul Farisy yace "Naga alama ta biyu".
Rannan kuma yazo wajen sai ya tarar Manzon Allah (saww) ya tashi domin rakiyar wata Jana'iza. Kuma alokacin nan Manzon Allah (saww) ya yafa wani bargo ajikinsa.
Don haka sai Salmanul Farisy yake ta bin bayan Manzon Allah (saww) yana ta lekawa ko zaiga Wannan Khatimin Annabtar...
Sai Manzon Allah (saww) ya zame bargonsa. Ya juya wajen Salmanul Farisiy yace masa "YA SALMANU, KO WANNAN ABIN KAKE SON GANI? ".
LAA ILAHA ILLAL LAAH!! ai lokacin da Salmanul Farisy ya kalli kyawu da hasken jikin Manzon Allah (saww) kuma ga Khatimin Annabtar nan atsakanin kafadunsa, Sai ya fashe da kuka!!
Ya rugume Manzon Allah (saww) yana ta kuka, yana sumbartar wannan Khatimin Annabtar!!!
Yana cewa "NA SHAIDA BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH, KUMA HAKIKA KAI MANZON ALLAH NE!!! "
GWARZON MUSULUNCI, SALMANUL FARISIY (RA) - KASHI NA 2
Tags:
Addini

0 comments: