An yi wani makaho a wani kauye da mutane ke fama da matsalar
wutar lantarki. A kauyen idan dare ya yi mutane kan kunna fitilarsu
su rika hira kafin su kwanta.
Wannan makahon yana da hazaka wajen wanke fitilarsa kowane
yammaci, da zarar gari ya yi duhu sai ya kunna ta. Ko da unguwa
zai je sai a gan shi rike da fitila.
Wannan al’amarin yana ba
mutanen kauyen mamaki sosai.
Wata rana da daddare ya fito daga gidansa rike da fitla kamar
yadda ya saba, sai ya hadu da wasu mutane suna wucewa a kan
hanya, daga nan suka rika tsokanarsa: “Haba malam makaho in
ban da rigimarka mene ne amfanin rike fitila, dare da rana duk
daya ne a wurinka. Kowa a kauyen nan ya san kai makaho ne,
amma ka rika yawo da fitila?”
Sai makaho ya ce musu “Ina rike wannan fitilar ne don masu
idanu, domin idan babu fitila ba za ku iya gani na ba, hakan zai sa
ku yi mini lahani. Amma idan kun gan ni rike da fitila za ku iya
taimaka mini, ko kuwa ku kauce idan na zo wucewa.” Sai abin ya
ba su tausayi, sannan kunya ta kama su, har suka ba shi hakuri.
WATAN RANA WANI MAKAHO
Tags:
Abin Mamaki

0 comments: