Akwai wani masunci da yake matukar son ‘ya’yansa ‘yan biyu,
Hassan da Hussaina, tun suna kanana mahaifiyarsu ta rasu. Hakan
ya sanya ya auro wata matar, sannan ya roki alfarmar ta rika lura
da su. Ta amince, amma abin da bai sani ba matar tasa ta tsani
‘ya’yansa.
Kullum da safe yakan shirya ya tafi kogi kamun kifi, inda ya fita ne
sai matarsa ta rika musguna wa ‘ya’yansa, sannan ta rika yi musu
barazanar kashe su idan suka fada wa mahaifinsu halin da ake ciki.
Hakan ya sa suka yi shiru, amma bayan wani lokaci sai mahaifinsu
ya fahimci halin da suke ciki. Ya kira matarsa ya yi mata nasiha,
amma al’amarin ya rika yin gaba.
Wata rana bayan ya tafi kogi sai matarsa ta dauki Hassan da
Hussaina, sannan ta kai su daji ta jefar, suka rasa hanyar dawowa,
haka suka ci gaba da tafiya ga yunwa, ga kishir ruwa, ga kuma
tsoro saboda dare ya fara yi, suna cikin tafiya ke nan sai suka iso
wata babbar bukkar mai cike da abinci da kuma kayan alatu, suka
yi murna, sannan suka ci abinci.
Bayan wani lokaci sai suka ga wata tsohuwa ta dawo, ashe mayya
ce. Daga nan dora tukunyar ruwan tsafi a murhu, sannan ta ce za
ta dafa su, ta cinye su. A lokacin da take iza wuta ne, sai Hassan ya
tura ta cikin tukunyar, ta fada cikin tukunyar ruwan zafi ya dafa ta,
haka ta mutu.
Daga nan suka gaji kayan alatu. Bayan sun dawo gida ne
mahaifinsu ya ga dukiyar da suka samu, sai ya rika farin ciki.
A karshe ya kori matarsa, bayan ya samu labarin abin da ta yi wa
‘ya’yansa.
Labarin Masunci da ‘ya’yansa
Tags:
Abin Mamaki

0 comments: