A wani lokaci da ya wuce an yi wani yaro da ake kira Kamilu. Yaro
ne mai ladabi da biyayya. Yana girmama na gaba da shi, sannan
ba ya raina na kasa da shi. Kowa yana yabonsa saboda kirkinsa.
Ba ya neman tsokana ballantana ya yi fada. Yana da hakuri tamkar
damo da ake yi wa kirarin sarkin hakuri.
Ana cikin haka ne wata rana ya je gona sai hadari ya taso, hakan
ya sanya ya kama hanyar dawowa gida, yana tafiya ne ya hadu
da wata tsohuwa dauke da wani kwando niki-niki tana tafiya da
kyar kamar za ta fadi.
Cikin sauri ya karbi tsohuwar bayan ya karasa wurinta. Daga nan
suka ci gaba da tafiya, inda aka fara yayyafi. Haka suka ci gaba da
tafiya har ya kai mata gidanta, sannan ya hura mata wuta saboda
ruwan da ya taba su lokacin suke kan hanya.
Tsohuwar ta ji dadi har sai ta ba shi kyautar Naira hamsin, amma
ya ki karba, ya ce mata ya yi ne don Allah.
Daga nan ta yi masa addu’a: “Allah Ya saka maka da alheri. Ya raba
ka da sharrin da ke cikin duniya.” Ya amsa, sannan ya fita.
Labarin Kamilu da Tsohuwa
Tags:
Abin Mamaki

0 comments: