Thursday, 6 November 2014

Labarin Yaro da Kunama

An yi wani lokaci akwai wani yaro marar ji, duk abin da aka fada
masa ba ya saurarar mutane. Ya cika rigima, komai ya gani sai ya
taba, ko kuma ya lalata. Mahaifiyarsa babu irin nasihar da ba ta yi
masa amma ya ki ji, wani lokaci har ta lakata masa duka amma
hakan ba zai hana ya ci gaba da rashin jinsa ba.
“Idan ba ka daina rashin ji ba, wata rana za ka hadu da gabanka, a
lokacin za ka dandana kudarka, za ka kuma fahimci lallai rashin ji
ba shi da amfani.” Inji mahaifiyarsa wata rana tana yi masa nasiha.
Amma bai saurare ta ba, ya fita waje yana guna-gunin ana takura
masa.


Wata rana ya zo zai sanya takalminsa, sai mahaifiyarsa ta ce masa
ya zazzage takalminsa, sannan ya share kafarsa kafin ya sanya
takalmin, amma ya yi kamar bai ji ta ba, zai sanya takalmin ke nan
ta sake fada masa, amma ya ki bin umarnin da ta yi masa.
Ashe abin da bai sani ba shi ne, akwai kunama a cikin takalmin,
bayan ya sanya ne ta harbe shi, a nan ya rika kuka, hankalin
mahaifiyarsa ya tashi bayan kunamar da ta harbe shi ta fito daga
cikin takalmin. Daga nan ta dauke shi zuwa wurin mai magani.


Bayan an yi masa magani sun dawo gida ne, sai ya rika tunanin
abin da ya yi bai kyauta ba, duk da haka mahaifiyarsa ba ta guje
shi ba, ta taimake shi duk rashin bin umarninta, ya yi nadama,
sannan ya roki gafara a wurin mahaifiyarsa. Ta yafe masa, tun
daga ranar bai kara ketare umarnin da mahaifiyarsa ba.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: