Thursday, 13 November 2014

RANAR KARBAR SAKAMAKON JARABAWA:

Ya kai 'Dan Uwa!! Shin ko ka ta'ba Lura da irin tashin hankalin da Dalibai suke shiga aduk lokacin da sakamakon Jarrabawa ya nuna cewa basu haye ba??


Wannan fa jarrabawa ce ta duniya, wacce koda ka fadi, ai kana da damar ka dawo ka gyara.


Shin wannan ba ya tuna maka da ranar da za'a Kafe sakamakon Jarrabawar Rayuwarka Gaba daya??


Ranar da Mutane zasu kasance rukuni biyu: Rukunin da zasu shiga Aljannah, sai kuma rukunin da zasu shiga Wuta. (Allah ya kiyayemu.)


Babu abinda yafi Gareni, dani da kai, da ke, da ku, Illa muYi kokari mu aikata ayyukan alkhairi masu yawa tare da kyautatuwar niyyah azuciya da kuma Tsoron Allah.


Ranar karbar sakamakon Jarrabawa tana nan zuwa babu makawa. Kuma babu wanda ya isa ya kauce ma afkuwarta.
Previous Post
Next Post

About Author

0 comments: