Wednesday, 7 October 2015

karanta wannan labarin a nutse

Watarana Wani Sarki Ya Kwanta Don Yayi Bacci Amma Sai Ya Kasa Yin Baccin Kuma Yaji Zuciyar Sa Sai Qunci Takeyi Ya Tsaya Yayi Nazari Don Yagano Dalilin Da Yasa Yake Jin Damuwa A Cikin Zuciyarsa Amma Sai Yakasa.

Kawai Sai Ya Fito Daga Cikin Gidan Sa Tare Da Mai Kula Da Gidan Shi Wato "Sarkin Gida" Suna Cikin Tafiya A Cikin 1 Daga Cikin Manyan Titin Garin Kawai Sai Suka Ga Gawar Wani Mutum Akwance Agefen Titi Kuma Jama'a Suna Ta Wucewa Gefen Gawar Amma Babu Wanda Ya Damu Da Gawar Ballatana Ayi Kokarin Yi Mata Jana'iza. A Lokacin Da Sarki Yaga Haka Sai Yayima Jama'a Magana Cewa Mai Nene Dalilin Da Yasa Suna Ganin Gawar Mutum A Gefen Titi Amma Sunki Sukula Da Ita Sai Jama'a Suka Ce Masa Ai Wannan Gawar Da Kake Gani Ba Kowa Bane Face (Wane Ne) Wanda Zindiqi Ne Bai Iya Komai Ba Sai Shan Giya Da Neman Matan Banza.

Sai Sarkin Yace: "Amma Dai Shima Yana Daga Cikin Al'ummar ANNABI S.A.W. Don Haka Dole Ataimaka Masa Don Haka Yanzu Ku Tsaya Mutaimaka Mu Kai Shi Gidansa Haka Dai Wasu Suka Tsaya Suka Dauke Shi Suka Kai Shi Gida" A Lokacin Da Suka Dauke Shi Suka Kai Shi Cikin Gida Sai Kowa Ya Watse Sai Sarkin Ne Da Dan Rakiyar Sa Suka Rage Sai Kuma Iyalan Ma'macin.

Babban Abinda Yaba Sarki Ma'maki Shine Yadda Yaga Matar Mamacin Nata Kuka Kuma Tana Yabon Mijinta Tana Cewa: "(Wane Kenan) Tunda Nake A Duniya Ban Ta6a Ganin Mutumin Kirki Ba Kamar Ka" Caraf Sai Sarkin Yace: "Mata To Yaya Akayi Ya Zama Mutumin Kirki"? Alhali Ga Jama'a Sai Aibatashi Sukeyi? Sai Matar Tace Masa Ai Suna Qyamarsa Ne Saboda A Tunanin Su Yana Shan Giya Kuma Yana Neman Matan Banza Amma Wani Abu Da Basu Sani Ba Shine A Duk Lokacin Da Yaje Gidan Giya Ya Siyo Giya Kwalba 3 Ko 4 To Idan Yazo Gida Ba Shan Giyar Yake Yiba A Cikin Masai (Bayan Gida/ Shadda) Yake Juyeta.

Sai Yace: "ALHAMDU LILLAH KO YANZU NA TAIMAKI AL'UMMAR MUSULMI TUNDA NARAGEMUSU SHARRIN DA YAKE BIBIYARSU" Sau Dayawa Miji Na Yana Zuwa Gidan Matan Banza Ya Sami Wata Suyi Ciniki Da Ita, Akan Cewa Yau Agidan Ta Zai Kwana Sannan Ya Biyata.

Amma Dare Nayi Sai Yaje Wajen Ta Ya Riqa Damunta Da Surutai Har Sai Dare Yaja Sosai Sai Ya Silale Yadawo Gida Sai Yace "ALHAMDU LILLAH KO YANZU DAI NA RAGEMA MATASAN MUSULMAI WANI BALA'I DA YAKE BIBIYARSU" Sau Dayawa A Lokacin Da Yana Raye Na Sha Gayamasa Ya Dai Na Wannan Dabi'a Don Gudun Kar Jama'a Suri Qa Qyamar Sa, Ko Kuma Ya Mutu Jama'a Suce Ba Za Suyi Masa Sallah Ba.

Shi Kuma Sai Yace: "Ai Allah S.W.T. Ya Sani Kuma Ko Da Makobta Na Basu Yimin Sallah Ba Toh Allah S.W.T. Zai Iya Kawo Mini Wa'yanda Zasu Yimin Sallah.

ko Da Sarki Yaji Haka Sai Ya Fashe Da Kuka. WANNAN KENAN

Sau Da Yawa Zakaga Muntsaya Muna Gulmar Wasu Daga Cikin Mu Wadanda Ke Aikata Wani Laifi Alhali Yin Hakan Babban Laifi Ne, Watakila Ma Yafi Laifin Wadanda Muke Gulmarsu Domin Ita Gulma Laifi Ne Guda 2 1. An Sa6ama Allah S.W.T. 2. Ko Da Katuba Toh Sai Ka Nemi Yafiyar Wanda Kayi Gulmar Sa Tukun. Alhali Watakila Wanda Mukeyin Gulmar Sa Laifin Sa Bai Kai Haka Girma Ba Don Haka Yakamata Mu Lura Da Kyau Sosai Akan Gulma. ALLAH S.W.T. YASA MUDACE Allah Ya Tsare Mu Da GulmaR Duniya Albarkan ANNABI MUHAMMADU Saw.

Previous Post
Next Post

About Author

5 comments: